Koriya ta Kudu ta ce, ta tura wasu jiragen yaƙi tare da kai harin jiragen yaƙi masu saukar ungulu a matsayin martani ga wasu jirage masara matuka na koriya ta Arewa da suka ratsa sararin samaniyarta
Ta ce harsasai kusan 100 aka harba amma sun kasa kakkaɓo ɗaya daga cikin jiragen.
Sojojin Koriya ta Kudu sun tsinkayi jiragen ne da safiyar yau Litinin da suka ratsa kan iyaka, kuma ɗaya daga cikinsu har ya ratso kusa da birnin Seoul babban birnin Koriya ta Kudun.
Lamarin da ya sa aka rufe wasu manyan filayen jiragen sama guda biyu a birnin.