A wani mataki na ramuwar gayya, Koriya ta Kudu ta harba makamai masu linzami takwas a gaɓar tekun gabashinta, a wani atisayen hadin gwiwa da Amurka.
An harba makaman ne a matsayin martani ga sabon gwajin makamin da Koriya ta Arewa ta yi a karshen mako.
Rundunar sojan Koriya ta Kudu ta ce tana so ne nuna makwabciyar tata cewa shiru-shiru ba wasa ba ne.
A ranar Lahadin da ta gabata ma, Pyongyang ta harba makamai masu linzami masu cin gajeren zango guda takwas cikin teku.
Hakan ya biyo bayan kammala atisayen sojin da Washington da Seoul suka yi a yankin.