Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yi wa Rasha tayin cikakken goyon bayan ƙasarsa a yaƙin Ukraine.
Ya bayyana haka ne a yayin tattaunawa da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da ke ziyara a Ukraine.
Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta wallafa wani bidiyo na ganawar da aka yi a birnin Wonsan.
Manazarta sun ce wataƙila Koriya ta Arewa tana shirin tura ƙarin dakaru domin taimaka wa Rasha a yaƙin da take a Ukraine.