Koriya ta Kudu da Japan sun ce, Koriya ta Arewa ta harba makamai biyu masu linzami daga gabar tekunta da ke gabashin ƙasar.
Japan ta ce tana zargin shu’umin makamin ya faɗa a wajen yanki na musamman da take harkokin kasuwancinta.
Kwamitin tsaro na MDD dai ya haramtawa Koriya ta Arewa gwajin irin wannan makami, da sauran ayyukan da suka shafi makaman nukilliya


