Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi, a ranar Laraba ya fito fili ƙarara ya bayyana cewa, a yanzu haka ya na shirin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Umahi ya bayyana wa manema labarai na cikin gidan gwamnati, bayan kammala taro da Buhari a fadar sa da ke Abuja, inda ya ce, a APC zai tsaya takarar.
Ya ce kamar yadda ya bayyana, saboda tsabar dagewar sa wurin son cika burin shi, har wadanda suke zawarcin kujerar tare sai da ya yi musu kamfen.
Yayin da aka tambaye shi idan ya hakura da takara, Umahi ya ce, zai yi wu tunanin wani ne hakan. Amma a iya sanin sa, ya na nan a kan bakar shi kuma masoyansa suna nan suna goya masa baya, yana ci gaba da kamfen kuma.