‘Yan bindiga sun kai hari gidan yarin Kuje da ke unguwar Kuje a babban birnin tarayya Abuja a daren ranar Talata.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa, ‘yan bindigar sun yi ta harbe-harbe ta kusan sa’a guda. Sun kuma bayyana cewa, an tashi bama-bamai a yayin harin.
Wata mai amfani da Twitter, Dara Moren, wadda ta ce, tana yankin a lokacin, ta yi wani rubutu game da harin.
“A yanzu haka a Kuje kuma an shafe kusan awa daya ana harbe-harbe. A ɗan kwantar da hankali kuma na gaba an sake fara harbe-harbe. Allah ya yi mana rahama,” kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.
“An kai hari gidan yarin Kuje! Fashewar bama-bamai biyu, harbe-harbe marasa adadi,” wani mai amfani, J.S. Ramadan kuma ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A wani labarin kuma, Ramadan ya yi zargin cewa fursunoni 15 ne suka tsere zuwa makarantar Sakandaren Gwamnati da ke yankin a yayin harin.
“Kimanin fursunoni 15 da suka fito daga gidan yarin Kuje ne suka kutsa cikin makarantar mu ta katanga. Dole ne mu kasance cikin sanyin gwiwa kuma mu ci gaba da yin addu’o’in neman lafiyarmu da kuma taimakon Allah mai yawa,” in ji Ramadan.