Akalla kasashe 14 ne suka tabbatar da samun gurbi a zagaye na 16 a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA da ke gudana a New Zealand da Australia, bayan kammala wasannin rukuni na ranar Laraba.
Afirka ta Kudu ta lallasa Italiya da ci 3-2, sannan Faransa ta samu nasara a kan Panama da ci 6-3, inda suka yi nasarar tsallakewa zuwa zagaye na 16. Jamaica ta yi kunnen doki da Brazil ci 0-0, Sweden kuma ta ci Argentina 2-0.
Hakan na nufin Sweden ta tsallake zuwa zagaye na 16 a matsayin ta daya a rukunin G da maki tara a wasanni uku, yayin da Jamaica kuma ta tsallake zuwa mataki na biyu a rukunin F.
Tuni dai kasashen Najeriya da Ingila da Denmark da Netherlands da Amurka da Japan da Spain suka samu tikitin shiga zagaye na 16 na karshe.
Sauran sune Australia, Norway, da Switzerland.
A gobe ne za a tantance kasashe biyu na karshe da za su sami maki biyu na karshe a cikin 16 na karshe.