Kodinetan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP na jihar Bauchi, kuma kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa, Rabi’u Kwankwaso, Babayo Liman ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Liman ya bayyana sauya shekar sa zuwa PDP ne a wani taron manema labarai jiya a Bauchi.
Sakataren jamâiyyar NNPP na shiyyar Arewa maso Gabas ya ce ya bar jamâiyyar ne saboda rashin tsarin da zai ci zabe.
Ya ce: âIna so in sanar da jamaâa a hukumance, musamman âyan jamâiyyar NNPP a jihar Bauchi da Arewa maso Gabas da Najeriya baki daya, cewa na yi murabus daga matsayina na dan jamâiyyar NNPP.
“Na kuma yi murabus daga mukamin sakataren shiyyar Arewa maso Gabas da kuma mamba kuma kodineta na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabiu Kwankwaso.”