fidelitybank

Kocin PSG Galtier na shan matsin lamba bayan kalaman wariyar launin fata da na addini

Date:

Kocin PSG Christophe Galtier na cikin matsala, bayan an yada kalamansa na nuna wariyar launin fata da kyamar Musulunci ga kafafen yada labarai.

Tsohon darektan kwallon kafa na OGC Nice Julien Fournier, a cikin imel, ya yi zarge-zarge a kan kocin Paris Saint-Germain, kuma ainihin imel ɗin ‘yan jarida Romain Molina da Daniel Riolo ne suka bayyana shi a ranar Talata.

Fournier ya aika imel ɗin zuwa INEOS (kamfanin da ke da Nice) darektan Dave Brailsford.

Sakon imel ɗin ya fallasa kalaman wariyar launin fata da Islama da Galtier ya yi a lokacin da yake a matsayin Manajan Nice, a cewar Sportskeeda.

Fournier, a cikin imel ɗin zuwa Brailsford, ya bayyana cewa, kocin ya bayyana rashin jin daɗin sa na samun ƴan wasa bakaken fata da musulmai da yawa a ƙungiyar.

“Ya (Christophe Galtier) ya gaya mani cewa dole ne in yi la’akari da ‘hakikanin birnin’ kuma ba za mu iya samun baƙar fata da Musulmai da yawa a cikin tawagar ba,” in ji imel a wani bangare.

Galtier ya kara bayyana a cikin sakon email din cewa, mutanen birnin Nice sun damu da cewa ‘yan wasa bakaken fata da musulmi ne suka karbe kungiyar duk da kasancewar birnin tsohon magajin garin Jacques Medecin, yana mai jaddada cewa, kungiyar ba ta nuna abin da mutane ke so ba. , “kamar yadda baya nuna kaina’.”

Tuni dai masu sha’awar kwallon kafa suka shiga shafukan sada zumunta suna yin Allah wadai da kalaman wariyar launin fata da kyamar Musulunci na Bafaranshen.

labaran duniya na yau

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp