Kocin Ghana, Otto Addo, ya ajiye aikinsa bayan da suka sha kashi a hannun Uruguay da ci 2-0 a wasansu na karshe na rukunin H a gasar cin kofin duniya.
Addo, wanda a baya ya nuna ba zai ci gaba da zama a kan mukamin ba bayan kammala gasar, ya tabbatar da cewa zai bar kungiyar bayan kammala gasar.
A cewarsa, yana so ya mai da hankali kan rawar da yake takawa tare da Borussia Dortmund a matsayin gwaninta.
“Na fadi hakan ne lokacin da na fara aiki a matsayin mataimakin [koci] a watan Oktoban bara. A bayyane yake cewa zan tsaya bayan gasar cin kofin duniya.
“A halin yanzu, ni da iyalina muna ganin makomarmu a Jamus. Ina son matsayina a [Borussia] Dortmund. Muna murna sosai a wurin.
“Na ce idan muka samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya zan yi murabus bayan komai, ko da kuwa mu ne zakarun duniya,” in ji Addo.
Wasan farko na Addo da ya jagoranci Black Stars shine wasan share fage da Najeriya.
Ghana dai ta yi kunnen doki ne babu ci a Kumasi kuma ta samu tikitin shiga gasar sakamakon 1-1 a Abuja.