Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Brazil, Tite, ya ajiye aikinsa bayan Croatia ta fitar da su daga Gasar Kofin Duniya a bugun finareti a wasan kwata fayinal da suka buga ranar Juma’a.
Kocin mai shekara 61, ya jagoranci Brazil tun daga 2016 kuma ya taɓa faɗa cewa zai bar aikin bayan gasar ta 2022 da ake yi a Qatar.
“Abin da ciwo amma na tafi ke nan. Ƙarshen lamarin ke nan a wajena,” kamar yadda ya faɗa wa ‘yan jarida bayan wasan da aka buga a filin wasa na Education City Stadium.
“Da ma na faɗi haka shekara ɗaya da ta wuce. Ban zo nan don na ci kofi ba kuma na ce zan ci gaba da aiki, waɗanda suka san ni sun san haka.”
Croatia ta doke Brazil 4-2 a bugun finareti bayan wasan ya tashi 1-1, inda ɗan wasa Neymar ya kamo Pele a yawan ci wa Brazil ƙwallaye da 75 kowannensu.
Akwai yiwuwar shi ma ɗan wasa Neymar ya jingine takalmansa saboda ya ce “babu tabbas ko zan sake buga wa Brazil wasa”.