fidelitybank

Kocin Atalanta ka yi wa Ademola kalamai na rashin mutunci – Okocha

Date:

Fitaccen dan wasan Najeriya, Austine ‘Jay Jay’ Okocha, ya caccaki manajan Atalanta, Gian Piero Gasperini saboda ” kalaman rashin mutunci” da ya yiwa Ademola Lookman.

Gasperini ya zayyana Lookman da laifin bayan La Dea ta doke Club Brugge da ci 3-1 a gasar zakarun Turai ranar Talata.

Lookman ya fito daga benci ya zura kwallo daya tilo da Atalanta ta ci a wasan, kuma ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida.

An fitar da kulob din Seria A daga gasar zakarun Turai bayan rashin nasara.

Wasu tsofaffin ‘yan wasan kwallon kafa da suka hada da Alessandro Del Piero da Samuel Eto’O sun bayyana goyon bayansu ga Lookman.

Okocha ya ce Gasperini ya fusata da kiran Lookman a matsayin “mafi munin mai daukar hukunci”

Mozzart Sport ta nakalto Okocha ya ce “Ina jin Gasperini ya wuce gona da iri ta hanyar kiran Lookman a matsayin mafi munin mai daukar fansa.”

“Da alama ya manta da irin gudunmawar da Lookman ya bayar ga Atalanta. Manyan ‘yan wasa da yawa sun rasa hukunci mai mahimmanci ba tare da fuskantar irin wannan kakkausar suka ba, to me yasa ake kula da batun Lookman daban? A ra’ayi na, idan kun fitar da Lookman daga Atalanta, kulob din zai iya yin gwagwarmaya har ma da hadarin komawa gasar. “

vanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp