Wasu daga cikin kwamishinonin gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel sun yi murabus a rana guda, ta Litinin, Maris 14, 2022.
Kwamishinonin biyu sun hada da Mista Akan Okon, wanda ya kasance kwamishinan raya tattalin arziki da tashar ruwan tekun Ibom da Fasto Sunny Ibuot mai kula da ci gaban kwadago da ma’aikata.
Akan Okon a cikin wasikar murabus din nasa ya godewa Emmanuel bisa wannan karramawa da kuma babbar gata da ya yi masa na yi wa jihar hidima, ya kara da cewa, zai ci gaba da godiya ga Allah Madaukakin Sarki da gwamnan da ya ba shi damar yin hidima.
Ya bayyana cewa, ya yanke shawarar barin Exco na jihar ne, saboda bukatar mayar da hankali kan burinsa na gwamna.
Ya kara da cewa yana fatan yiwa jihar hidima a matsayin gwamna a shekarar 2023, ya na mai jaddada cewa, akwai lokaci a kowace kakar kamar yadda nassi ya gargadi.
“Ina da yakinin cewa wannan ne lokacin da ya fi dacewa da zan tafi hutu, domin mayar da hankali kan burina na zaben Gwamna a 2023,” in ji shi.