fidelitybank

Ko mai Buhari ya ce a kan wahalar man fetur a Najeriya?

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa mutanen kasar hakuri kan matsalar rashin wuta da wahalar fetur da ake fama da su.

Cikin wata sanarwa da shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ba ya jin daÉ—in halin dogon layin da ‘yan kasar ke ciki na man fetur, “wani abu da gwamnatinmu ta yi kokarin kawarwa cikin shekaru bakwan da muka yi a ofis”.

Ya kara da cewa hakuri ne da ake bai wa duka sassan Najeriya baki daya.

Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da matsalar rashin wuta da ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a Najeriya.

“Gwamnatinmu na aiki ba dare ba rana domin ganin an kawo karshen wannan matsala. Kuma shirin da aka tsara a farkon wannan wata za a aiwatar da shi domin tabbatar da an kawo karshen karancin man da ake fama da shi,” in ji sanarwar.

Za a ci gaba da kawo isasshen mai a ko wacce jiha kamar yadda ake yi a baya, domin kawo karshen layin da ake fama da shi a fadin kasar.

Duk da cewa ana fama da matsalar koma baya a kasuwar makamashi ta duniya a wadannan watannin, kuma gwamnati za ta yi abin da za ta yi domin tabbatar da cewa masu amfani da man masu samu matsalar farashin man da ake fama da shi a duniya.

“Na samu labarin cewa wasu mutane da yawa na abubuwan da ba su dace ba a defo-defo na dauko mai ciki har da masu gidajen mai.

“Kuma na bayar da umarni ga ma’aikatar man fetur da albarkatun kasa da NNPC da sauran jami’an tsaro su dauki mataki kan duk wadanda aka kama da wannan ta’ada”, in ji Buhari

www.nigeriannewspapers.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp