An haifi Trump a Queens da ke birnin New York a shekara 1946. Ya taso ne cikin kasuwancin gidaje da ya gada daga mahaifinsa Fred Trump.
Bayan ya kammala makarantar soji, sai Trump ya shiga harkokin kasuwancin mahaifinsa, inda ya karɓi ragamar kasuwancin tare da faɗaɗa shi.
Filayen wasan golf da manyan otel-otel da sauran wuraren nishaɗinsu suna nuna alamomin arziki da isa. Amma shi Trump burinsa ya wuce kasuwancin.
A shekarar 2004, ya fara gabatar da shirin talabijin mai suna ‘The Apprentice’. A cewar BBC.