fidelitybank

Ko kun san dan shugaban Laberia George Weah shi ya zura wa Amurka kwallo a Qatar

Date:

Timothy Weah, wanda da ne ga Shugaban Liberia kuma tsohon dan kwallon duniya George Weah, ya ci wa Amurka kwallo a wasansu da Wales ranar Litinin.

Kasashen biyu sun tashi kunnen-doki 1-1, a wasa na biyu a rukunin B a ci gaba da gasar cin kofin duniya da ake yi a Qatar.

Yanzu haka Shugaba Weah na Qatar don kallon dansa wanda ya haifa a Amurka wato Tim Weah.

Sai dai Shugaban na shan suka, bayan da ministan kudin kasarsa ya ce za a rika bai wa Shugaban dala 2,000 a kullum a matsayin alawus har tsawon kwanaki tara da zai yi a Qatar.

Masu suka sun ce hakan ya yi hannun riga da alkawarin da ya dauka na rage kudin da ake kashewa wurin gudanar da gwamnati saboda inganta rayuwar talaka.

Geoge Weah ya kafa tarihi a matsayin dan kwallo daya tilo daga nahiyar Afrika, da ya taba lashe kyautar dan kwallon duniya ta Ballon D’or a ranar 24 ga watan Disamban 1995.

hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Za mu ladabtar da Jami’an mu da aka gansu suna taimakawa ‘yan siyasa a Kano – ‘Yansanda

Rundunar Æ´an sanda ta jihar Kano ta ce, ta...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...
X whatsapp