Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra, ya yi barazana ga ‘yan mazabar sa da su zabi ‘yan takarar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA kawai, ko kuma su kasa samun kulawa daga gare shi.
A cikin wani faifan bidiyo da ya ke zagayawa a kafafen sada zumunta, an ga Soludo yana shaida wa ‘yan mazabar Igbo-Uwku/Aguata 2 cewa idan suka zabi wani daga wata jam’iyya ba APGA ba, albashi ne kawai zai biya shi.
Gwamnan ya kuma ce abokinsa ne kawai wanda yake jam’iyyar siyasa daya ne zai samu damar zuwa wurinsa.
Karanta Wannan: Lado bai janye daga takarar gwamna ba a Katsina – PDP
“Duk mutumin da zan yi aiki da shi dole ya zama APGA. Idan ka zabi wani ya ci nasara ya hau Awka, ka tabbatar da albashi kawai yake karba. Idan ya karbi albashinsa zai koma gida.
“Ba wanda ke gina tituna a Majalisar; ba ya gina asibitoci ko makarantu domin ba shi da kudi. Ni gwamna, ni kadai ne zan iya yin dukkan wadannan abubuwan. Kuma wanda abokina ne kuma dan jam’iyyar siyasa daya ne kawai zai samu damar zuwa wurina. Irin wannan mutum ne kawai zai iya ba ni shawara a kan waɗannan ayyukan da za a yi.
“Eh, haka yakamata ya kasance. Nawa ne kawai zan amsa duk lokacin da ya kira ya ji. Idan ka kawo wani daga wata jam’iyya, albashi za mu rika biyansa ne kawai. Kuma a gargade shi kada ya zo kusa da ni ya ce in yi wa jama’arsa komai. Kada ya kuskura,” in ji Soludo.