Dan majalisar wakilai, Alhassan Ado-Doguwa, ya yi barazanar yiwa ‘yan mazabar sa cewa ko dai su zabi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar zabe ko kuma a yi maganinsu.
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai na neman komawa majalisar a karo na bakwai.
Yana wakiltar mazabar Doguwa/Tudun-Wada a jihar Kano.
Jaridar Daily Nigerian ta yi ikirarin cewa ta samu wani faifan bidiyo a ranar Litinin da ta gabata, wanda ke nuna Doguwa na yin wannan barazana a wani gangamin siyasa a Kano.
A cewar rahoton, Doguwa ya fi magana da harshen Hausa, sannan ya kuma yi amfani da kalaman batanci wajen yin barazana ga masu son kada kuri’a.
“Ga Allah da ya yi ni, ranar zabe, ku zabi APC ko mu yi maganin ku.
“Ina sake cewa: a ranar zabe ko dai ku zabi APC, ko kuma mu yi maganin ku.
“Maimaita bayana, a Doguwa ko dai ku zabi APC ko kuma mu yi maganin ku,” in ji shi a cikin yabo da jama’a suka yi.