fidelitybank

Ko kadan ba zamu raga wa ‘yan bindiga ba – Buhari

Date:

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kara nanata aniyar gwamnatinsa na kawo karshen matsalar tsaron da kasar ke fuskanta, yana mai cewa, ko kadan ba zai raga wa ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare a fadin kasar.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi, ya ce manyan hafsoshin tsaron kasar na iya bakin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen matsalar ‘yan bindiga a kasar.

Ya kuma jajanta wa tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Adamu Muazu, saboda kashe dan uwansa da ‘yan bindiga suka yi tare kuma da kame ‘yar uwarsa.

Yayin da yake bayyana ‘yan bindigar a matsayin makiya al’uma, Shugaba Buhari ya ce, ya kadu matuka da wannan kisan

Ya kara da cewa ”Na yi matukar kaduwa da jijn labarin kashe dan uwanka, tare da kama ‘yar uwarka. Wannan masifa kullum karuwa take yi a kasar nan. Na sani kuna cikin halin damuwa, ina taya ku bakin-ciki”

”Matsalar tsaro ita ce babban abin da na sa a gaba, na kuma umarci manyan hafsoshin tsaron kasar da su yi iya bakin kokarinsu, domin kawo karshen wannan matsala da kasarmu ke ciki’‘. In ji Buhari

Wadannan kalaman na zuwa ne bayan ‘yan bindigar da suka sace gomman fasinjojin jirgin kasan nan na Abuja zuwa Kaduna, tun ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata, sun sake fitar da wani sabon hoton bidiyo da ke nuna mutanen da ake garkuwa da su cikin mummunan yanayi.

A cikin bidiyon mai tsawon kusan minti goma sha daya, an ga ‘yan bindigar na lakada wa fasinjojin maza dukan tsiya da ita ce.

vanguardnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp