Biyo bayan sauya sheka da ‘ya’yan jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki ke yi a baya-bayan nan, shugabanta na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce jam’iyyar ba za ta iya tilasta wa kowane dan jam’iyyar tsayawa ko ficewa ba.
Adamu, ya yi alfahari da cewa ko da mutane sun fice daga jam’iyyar, za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bayyana haka ne bayan ya ziyarci gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule a gidan gwamnati dake Lafia.
SaharaReporters ta ruwaito, tun a ranar Lahadi bayan da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu ya bayyana Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa, dan uwa musulmi ne wasu ‘yan jam’iyyar suka yi murabus daga mukaminsu.
Haka kuma an sha yin tofin Allah tsine a duk fadin kasar, musamman ma mabiya addinin kirista dangane da matakin da jam’iyyar ta dauka na gudanar da tikitin takarar shugaban kasa na musulmi da musulmi.
Sai dai Adamu ya ce, duk da cewa ba za su so kowa ya fice daga jam’iyyar ba, hakan ba zai hana kowa ba.
Ya ce, “Ba ma so mu rasa wani mamba amma idan da gangan dan mamba yana son ficewa daga jam’iyyar ba tare da neman mafita ba, ba za mu iya tilasta wa kowa ya tsaya ko barin jam’iyyar ba.
“Batun sauya sheka, akwai lokacinsa a siyasa musamman a kasashe masu tasowa, kuma ba sabon abu bane a Najeriya.
“Duk wanda yake cikin wannan jam’iyya babba ne kuma idan babba ya yanke shawara, to ko dai ka gamsar da shi, idan kuma hukuncin bai dace da kai ba, kuma ya aikata abin da ya umarta, to ka bar shi ga Allah shi ne ya tsara komai.