Hukumar zaɓen mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC) ta ce ta kammala shiryawa tsaf! domin gudanar zaɓukan ƙananan hukumomin jihar a yau Asabar.
Rundunar ‘yansandan jihar ta ce ba za ta samar da tsaro ba a lokacin zaɓen, saboda yin biyayya ga umarnin kotu.
A cikin makon da ya gabatan ne dai wata babbar kotun tarayya a Abuja ta bayar da umarnin ɗage zaɓen.
Lamarin da ya sa jam’iyyar PDP da APC a jihar suka gudanar da zanga-zanga tare da ƙaurace wa zaɓen.
To sai dai hukumar zaɓen jihar ta nuna rashin amincewarta da hukuncin kotun, sakamkon samun hukuncin wata babbar kotun jihar Rivers.
Jami’in hulɗa da jama’a da wayar da kan masu zaɓe na hukumar, Tobin Tamunotonye ya hukumar zabe za ta gudanar da zaɓukan na yau ba gudu ba ja da baya.