Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, ya bayyana cewa, ko ta yaya sai jam’iyyar APC ta yi fatali da PDP a zaben 2023.
Agege na cikin masu neman takarar gwamnan jam’iyyar Delta a zaben 2023 karkashin jam’iyyar APC.
A gefe guda, Sanata Nwaboshi wanda bai dade da komawa APC ba ya ce babu lungun magudi da bai sani ba.
Omo-Agege ya bayyana hakan ne a bikin rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar APC, reshen jihar Delta, in ji Vanguard.