Kocin Liverpool Jurgen Klopp, ya caccaki tsohon dan wasan Aston Villa, Gabriel Agbonlahor, kan kalaman da ya yi a kan Manchester United.
Bayan kashin da Manchester United ta sha a hannun Brentford da ci 4-0 a karshen makon da ya gabata, Agbonlahor ya gayawa Manchester United kalamai marasa dadi, amma Klopp ya tsawatar da tsohon dan wasan na Aston Villa.
Klopp ya ce, yana sauraron shirin a talkSPORT lokacin da Agbonlahor ke yanka tawagar Erik ten Hag, kuma ya tunatar da tsohon dan wasan cewa, Liverpool ta taba doke Aston da ci 6-0 yayin da Agbonlahor ke taka rawar gani a fagen kwallon kafa, kuma shi ne kyaftin din kungiyar ta Villa.
“Na koma gida bayan na kalli wasan farko a nan ( filin atisayen Liverpool). Na saurari talkSPORT kuma na ji Gabby Agbonlahor. Abin da ya ce game da United abu ne da ba za a iya yarda da shi ba,” Bajamushen ya shaida wa talkSPORT.
“Ya yi rashin nasara da ci 6-0 a nan Villa a kakar wasa ta farko. Shi ba dodo ba ne a wannan wasan. Na kusa kira.”


