Tauraron dan wasan Senegal, Salif Diao ya zargi Jurgen Klopp da laifin tafiyar Sadio Mane daga Liverpool a wannan bazarar.
A cewar Diao, Klopp bai nuna wa dan kasarsa isashen soyayya ba.
Mane ya bar kungiyar ta Reds bayan ya shafe shekaru shida a Anfield inda ya koma Bayern Munich.
A lokacin da ya yi a can, Mane ko da yaushe kamar yana wasa na biyu ga Mohamed Salah.
Yarjejeniyar Salah dai za ta kare ne a watan Yunin 2023, amma kungiyar ta Premier ta yi yaki sosai don ganin ta ci gaba da rike dan wasan na Masar, ta hanyar mayar da shi dan wasan da ya fi karbar albashi a tarihinsu.
Amma an bar Mane ya tafi, yayin da Klopp ya kawo Darwin Nunez daga Benfica.
“Ina tsammanin ya kasance a nan tsawon shekaru biyu kuma ina tsammanin a wani lokaci ya yi tunanin ba shi da soyayyar da yake bukata da gaske, a nan Anfield.
“Ba na magana game da magoya baya, a gare shi ina tsammanin ya fi dacewa da kocin,” Diao ya shaida wa Liverpool Echo.