Jim kaɗan bayan kama aiki, sabon ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya sha alwashin kawo karshen kiwon sake a Abuja.
Ministan ya kuma ce zai tuntuɓi makiyayan a kan wannan batu.
Wike ya bayyana haka ne lokacin ganawa da manema labarai a ranarsa ta farko a ofis, yayin da ya sha alwashin tsaftace Babban Birnin Tarayyar.
Sabon ministan ya ce makiyaya za su iya kiwon shanu a wajen birnin amma kuma ba za a bari su ci ciyawar da ake amfani da ita wajen ƙawata birnin ba.
“Za mu tuntubi makiyayan domin mu ga yadda za mu daina kiwon sake saboda ba za mu iya barin shanu a cikin garin Abuja ba,” in ji shi.
Wike ya ce an dasa ciyayin ne a birnin domin ƙawata shi ba domin shanu su ci ko su ɓata ba.