Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta kama Maryam Habibu, ‘yar shekara 18 da haihuwa, bisa zarginta da jefa ɗan kishiyarta mai shekaru hudu a cikin rijiya da ke karamar hukumar Kafur ta jihar.
Maryam Habibu waddat ta fito daga kauyen Leko da ke karamar hukumar Danja tare da wasu mutane 11 da ake tuhuma da laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami da satar shanu, an gurfanar da su a ranar Juma’a a hedikwatar ‘yan sanda da ke Katsina.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, yayin da yake zantawa da manema labarai yayin holin ya bayyana cewa, an kama matar ne a ranar 9 ga Nuwamba, 2022.
Ya ci gaba da bayyana cewar ta fitar da yaron ne ta jefa shi cikin rijiya.
A cewar jami’in hulda da jama’a, Maryam Habibu da mahaifin wanda aka kashen sun kasance ba sa tare.
Maryam Habibu wanda ta zanta da manema labarai ta amince da aikata laifin, ta na mai cewa kaddara ce.
A cewarta, “Gaskiya ne na jefa yaron a cikin rijiyar da ya mutu amma an kaddara cewa zai mutu a ranar. Shi ya sa ya rasu.”