fidelitybank

Kisan Nabeehah a hannun masu garkuwa ya fusata ‘yan kasa

Date:

Bayanai na cewa ɗaya daga cikin ƴan mata shida da aka yi garkuwa da su a Abuja tun mako ɗaya da ya gabata ta mutu a hannun masu garkuwa da su lamarin da ya fusata jama’a a ƙasar nan.

Ƴan bindiga ne suka yi dirar mikiya a gidansu da ke yankin Bwari a Abuja tare da harbe ƴan sanda uku kafin daga bisani su yi garkuwa da ƴan matan da mahaifinsu.

A cewar rahotanni, ƴan bindigar sun halaka Nabeehah – ɗaya daga cikin ƴan matan a ƙarshen mako wadda ɗaliba ce a jami’a bayan da danginta suka gaza biyan kuɗin fansa.

Wani ɗan uwan ƴan matan ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ƴan bindigar sun miƙa wa ƴan uwan Nabeehah gawarta.

Ƴan bindigar dai sun yi barazanar halaka ƴan uwan Nabeehah da ke hannunsu idan ba a biya su kuɗin fansa ba nan da ranar Laraba.

Biyu daga cikin ƴan sanda uku da ƴan bindigar suka harba a lokacin da suka kai hari suma sun mutu kamar yadda rahotanni ke bayyanawa.

Ƴan sanda sun ce suna yin duk mai yiwuwa domin kuɓutar da ƴan matan sai dai ba su tabbatar da mutuwar Nabeehah ba.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ya ce kisan Nabeehah wata tunatarwa ce cewa ƴan bindiga na cin karensu ba babbaka a ƙasar inda kuma ya yi kira a kawo gyara a harkokin tsaron ƙasar.

Shi ma Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar Labour ya ce batun garkuwa a babban birnin ƙasar manuniya ce kan rashin tsaro a sauran sassan ƙasar.

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp