fidelitybank

Kisan Matashi: Ba za mu iya jure irin mummunan aikin ba – Kungiyar Miyetti

Date:

Kungiyar Miyetti Allah ta Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) ta tabbatar da harbe wani makiyayi dan shekara 14 mai suna Idris Idris a unguwar Dong da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.

A cewar shugaban kungiyar na jihar, Malam Nura Abdullahi, ya ce an kashe marigayin ne da yammacin ranar Asabar.

Ya ce“An kai masa hari ne a lokacin da yake kiwon dabbobi, amma ba a kashe saniya ba ko daya ba. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:pm. Makiyayan biyu ne, amma daya ya tsira daga harin. Mun kai rahoto ga DPO na shelkwatar ‘yan sandan karamar hukumar Bassa.

“Babu hujjar kisan, saboda mamacin ya na kiwon shanu ne kawai. Me ya yi da ya cancanci a kashe shi? Ba za mu iya ci gaba da jure wa irin wannan mummunan aiki ba. Muna kira ga jami’an tsaro da su yi abin da ya dace a kai, domin kamo wadanda suka aikata wannan aika aika.” In jiNura Abdullahi.

Mun kuma tuntubi mai magana da yawun rundunar ’Yan sandan Jihar, ASP Ubah Gaberiel, game da faruwar lamarin, bai amsa kiran da wakilinmu ya yi masa ba.

vanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp