fidelitybank

Kisan Lafiya: Gwamnan Legas ya gana da Shugaban ƴan sanda

Date:

Babban Sifeton ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya gana da gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu a shelkwatar hukumar ‘yan sandan ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar, domin tattauna wasu batutuwa ciki har da batun yin adalci ga lauyar nan da wani jami’an ɗan sanda ya harbe a birnin Legas ranar Kirsimeti.

A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ya ce babban sifeton ‘yan sandan, ya jadda cewa za a gudanar da cikakken bincike tare da alƙawarin yin adalci game da batun, yana mai cewa hukumar na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ofishin babban lauyan gwamnatin jihar Legas domin tabbatar da an gurfanar da wanda ke da hannu a gaban kotu.

A nasa ɓangare gwamnan jihar Legas ɗin ya alkawarta taimaka wa rundunar ‘yan sandan domin ganin cewa an yi adalci game da binciken kisan lauyar.

Tuni dai babban Sifeton ‘yan Sandan ƙasar ya bayar da umarnin dakatar da jami’in ɗan sandan da ya harbe tare da kashe lauyar mai suna Omobolanle Raheem a birnin Legas.

uanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...

NNPP ta yi tafka magudi a zabencike gurbin Kano – Farouk Lawan

Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi zargin...

Dan shugaban kungiyar Boko Haram ya shiga hannu

Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama yaron shugaban ƙungiyar...
X whatsapp