fidelitybank

Kisan kiyashi Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa zan ayyana ku a matsayin yaƙi ƙarara – Turkiyya

Date:

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya kira hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza da ”kisan kiyashi”.

Yayin da yake jawabi cincirindon mutane a birnin santambul, Mista Erdogan ya ce ƙasashen yamma ƙawayen Isra’ila su ne ke ingizata wajen aikata abin da ya kira “laifukan yaƙi”.

“Isra’ila, za mu ayyana ki a matsayin mai aikata laifukan yaƙi a duniya. Muna shirin yin haka, kuma za mu gabatar da Isra’ila ga duniya a matsayin mai aikata laifukan yaƙi”, in ji Erdogan.

Shugaban na Turkiya ya ci gaba da kare matsayinsa na ƙin amincewa da ayyana Hamas a matsayin “ƙungiyar ta’addanci”.

Matsayin da ƙasashen Amurka da Birntaniya da wasu wuraren suka ɗauka kan ƙungiyar.

Erdogan na jawabin ne a gaban taron ɗimbin jama’a da ya ce sun kai mutum miliyan 1.5

Waɗanda suka halarci taron sun riƙe tutar Falasdinawa da ta ƙasar Turkiya.

Taron – wanda aka kira babban tattakin goyon bayan Falasɗinawa – an gudanar da shi ne a filin jirgin sama na Ataturk, inda Erdogan ke gudanar da gangaminsa a baya-bayan nan.

A ranar Asabar, ya sake nanata sukarsa ga ƙasashen Yamma, kan ƙin kiran tsagaita wuta a Gaza.

Shugaban na Turkiyya ya kuma kira ƙasashen musulmai na duniya da su haɗa kai.

daily 
post news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp