fidelitybank

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Date:

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare da kiran gwamnati ta ɗauki cikin gaggawa domin kawo ƙarshen kashe-kashen.

Tsohon ɗan takarar shuagaban ƙasar na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya nuna damuwa matuka kan ci gaba da zubar da jini a jihar Benue, yana mai kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa domin kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar yankin.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana halin da ake ciki a matsayin “mummunar masifa” da gwamnatin ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kai.

Atiku ya ce al’ummar Benue na fama da hare-hare na tsawon shekaru, inda rayuka ke salwanta, kauyuka ke lalacewa, iyalai ke rasa muhallansu.

“Buƙatarmu ita ce samun zaman lafiya da noma ba tare da fargabar mutuwa ba, da kuma tarbiyyar ‘ya’yansu cikin kwanciyar hankali.” in ji Atiku.

Ya jaddada cewa wadannan hakkoki ne da ƙundin tsarin mulki na kasa ya tanada, kuma wajibi ne gwamnati ta kare su.

Ya kuma yi Allah-wadai da yadda jami’an tsaro ke amfani da karfi da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar lumana a Benue da ke neman kariya daga gwamnati.

“Hakan ba salon mulki ba ne, illa zalunci ne da cin amanar shugabanci.” Ya ce hakan yana nuna yadda gwamnati ta yi biris da kukan jama’a.

Atiku ya ƙara da cewa matsalar tsaro ba a Benue kaɗai take ba, har da jihohin Plateau da Zamfara da Kaduna da kuma Taraba, inda jama’a ke fuskantar irin wannan hali.

Ya bukaci shuwagabanni da gwamnatocin jihohi da su mayar da hankali kan kare rayukan ‘yan ƙasa fiye da yin fito na fito da siyasa, ta hanyar aiki da hukumomin tsaro da samar da kayan aiki masu inganci ga yankunan da abin ya shafa.

Hakazalika, Atiku ya yi kira ga ƴan Najeriya da kada su yi shiru a gaban zalunci. Ya bukace su da su ɗaga murya su nemi adalci da aukar mataki.

legit.ng.news.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...
X whatsapp