Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi ga ƴan Najeriya su ƙara haƙuri, inda ta ce lallai akwai haske a gaba.
Oluremi ta bayyana haka ne a saƙonta na Kirsimeti ga ƴan Najeriya, inda ta ƙara da godiya da ƴan Najeriya bisa haƙurinsu da goyon bayan da suke bayarwa wajen gina Najeriya.
A cewartsa, “ina tabbatar muku cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a shirye yake ya kawo gyare-gyare da za su inganta rayuwar ƴan Najeriya, waɗanda tuni wasu daga cikin sun fara nuna alamar nasara.
“Mu cigaba da ƙarfafa gwiwar juna, da haɗin kai domin inganta ƙasarmu.”