Dan wasan baya na Argentina, Cristian Romero ya radawa sabon jaririn sa suna Valentine sakamakon haihuwa da matar sa Karen Cavaller da ta yi.
Ma’auratan sun sanar da zuwan jaririn ta hanyar shafukan sada zumunta a ranar Alhamis, 23 ga Disamba, 2021.
Romero wanda yak e taka leda a Tottenham Hotspur ta yi nasara a kan West Ham United da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da na karshe na gasar Premier Carabao da aka buga ranar Laraba, 22 ga Disamba, 2021.
Matashin mai shekaru 23 ya yi amfani da shafinsa na Instagram inda ya sanya hoton matarsa da sabon jaririn.
A cikin faifan bidiyon, an ga abokiyar zamansa Karen rike da jaririn. Tare da wani hoto akwai sakon da ya bayyana sunan jaririn a matsayin Valentine.
Sakon ya ce, “Barka da safiya soyayya @karencavaller Barka da Valentine, muna jiran ku son rayuwarmu.”
Romero ya koma Tottenham ne a matsayin aro daga kungiyar Atalanta ta Italiya kuma har yanzu bai taka leda a karkashin Antonio Conte ba.