Kwamishinan kula da yawan jama’a na kasa, Dakta Abdulmalik Durunguwa, ya bayyana fatansa na ganin cewa, kidayar jama’a a shekarar 2023 za ta magance dimbin kalubalen da ke addabar kasar nan.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja, ya bayar da tabbacin cewa, za a magance galibin matsalolin da ke addabar kasar idan an gudanar da kidayar jama’a sosai, yana mai cewa aikin zai nuna wa gwamnati hanyar da za ta bi wajen magance matsalolin.
A cewarsa, “kidayar za ta samar da bayanan da ake bukata ga gwamnati da abokan huldar ta don tsara yadda za a biya bukatun jama’a da kuma yadda za a dora kasar nan kan turbar ci gaba mai dorewa.”
Ya kara da cewa bayanan da ake bukata shine sanin inda mutum yake ba wai kauye ko jiha ba, yana mai jaddada cewa ainihin bayanan shine magance matsalolin mutane.
Ya bayyana cewa kasar na bukatar sanin abubuwan da suka hada da yadda al’ummarta ke ciki don haka ya kamata a kirga mutane a duk inda suke.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su tabbatar an kidaya su domin gwamnati ta san mutanen da za su taimaka da yadda gwamnati za ta tsara.
Gwamnati, bayan kidayar, a cewarsa, za ta samu takardar aiki da za a yi amfani da ita wajen magance kalubale na musamman da ke shafar mutanen da ke zaune a sassan kasar.