Ma’aikatar harkokin waje ta ƙasar Senegal ta ce, kiran da ƙasar Ukraine ta yi na neman tallafin sojojin sa-kai a yaƙin da take yi da Rasha ya saɓawa dokokin Senegal.
Wata sanarwa daga ma’aikatar ta ce, ɗaukar sojojin haya da na sa-kai da ma sauran mayaƙa ya saɓa wa dokokin ƙasar.
Hukumomi sun kira jekadan Ukraine a Senegal, Yurii Pyvovarov, don ya yi musu ƙarin bayani game da shelar da suka yi a Facebook. Bayan an tabbatar da ingancin shelar, an nemi jekadan ya goge sanarwar.
Sai dai ba a bayyana ba, ko hukumomin Senegal za su ɗauki wani ƙarin mataki.
Senegal na cikin ƙasashen Afirka 17 da suka ƙaurace wa kaɗa ƙuri’a, domin yin Allah wadai da hare-haren Rasha a Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD). A cewar BBC.