Babban hafsan tsaron kasa (CDS), Janar Lucky Irabor, ya caccaki kiran da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi kan al’ummar jihar cewa da su dauki makamai domin kare kansu daga ‘yan bindiga.
Irabor ya ce, kiran bai yi dai-dai ba, domin kuwa jami’an tsaro da sauran jami’an tsaro na can domin tunkarar kalubalen.
Irabor ya zanta da manema labarai kan lamarin a wajen bude taron hadin gwiwa na kwalejin tsaro ta kasa da kwalejojin yaki na rundunar sojin Najeriya mai lamba “Exercise Grand Nationale,” a Abuja.
Irabor ya ce, har yanzu bai fahimci dalilin da ya sa ‘yan jihar Zamfara su dauki makamai ba.
Sai dai ya ce hakki ne da ya rataya a wuyan Babban Lauyan Tarayya ya duba kundin tsarin mulki da dokoki don ganin ko gwamnan yana da irin wannan iko.
“Na yi imani cewa, a ganina, ba hanya ce da ta dace ba.
“Tabbas akwai ayyuka da jami’an tsaro da na sojoji, musamman ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suke yi na magance tashe-tashen hankula a Zamfara da kewaye.
“Bayan haka, ko shakka babu, akwai wasu batutuwan shari’a, da sauran batutuwan da suka shafi mulki, batutuwan da gwamnati za ta iya magance su ta hanyar amfani da kayan aikin doka da aka tanadar masa domin samar da zaman lafiya da tsaro.