fidelitybank

Kifewar kwale-kwale yayi sanadiyar mutuwar mutane 33 a Neja

Date:

Akalla mutum 33 wadanda suka hada da mata da kananan yara ne ake tunanin sun mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale da ke dauke da fasinjoji fiye da 50 a kogin Kaduna a jihar Naija.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa kwale-kwalen ya taso ne daga kauyen Danchitagi da ke karamar hukumar Lavun zuwa kauyen Gbara da ke karamar hukumar Mokwa a jihar ta Naija ranar Juma’a da daddare.

Rahotonni sun ruwaito cewa hatsarin ya faru ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska mai karfin gaske.

Tuni dai aka dauki wadanda aka kubutar zuwa asibitin kauyen Gbara domin ba su kulawar gaggawa.

Hatsarin kwale-kwale dai na neman zama ruwan dare a Najeriya, ko a ranar Litinin din da ta gabata ma a ƙalla mutum 76 ne aka bayar da rahoton mutuwarsu bayan hatsarin kwale-kwale a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Kwale-kwalen, wanda ke É—auke da mutum 80, ya kife a yankin Ogbaru da ke jihar Anambran.

Mafi yawan wadanda abin ya rutsa da su mata ne da yara, da ke ƙoƙarin tsere wa yankinsu da ambliyar ruwa ta mamaye.

nan news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp