fidelitybank

Kenya ta kori dan Najeriya da ya ci zarafin Budurwarsa Gurguwa

Date:

Ƙasar Kenya ta kori ɗan Najeriyar da aka gani a cikin wani bidiyio yana dukan abokinyar zamansa da ke zaune a kan keken guragu.

A ranar Asabar 4 ga watan Mayu ne aka fitar da ɗan Najeriyar, mai suna Nwankwo Noko daga Kenya, bayan ya daki budurwar tasa mai suna Pauline.

Kyamarar tsaro ta CCTV ce ta ɗauki hoton Noko a lokacin da yake tsaka da bugun matar ‘yan asalin Kenya da ke amfani da keken guragu.

Da alama lamarin ya faru ne gidansu, A cikin bidiyon an ga mutumin na dukan abokiyar zaman tasa kafin wasu mata biyu su kawo mata ɗauki.

Ranar 29 ga watan Afrilu ne bidiyon ya karaɗe shafukan sada zumunta, lamarin da ya sa zaɓaɓɓiyar sanatar yankin Gloria Orwoba ta shiga cikin batun.

‘Yar majalisar ta gana da matar ranar 1 ga watan Mayu, sannan kuma aka kai ƙorafi zuwa ofishin ‘yan sanda na Karen.

”Mutane ba sa iya kai ƙorafin cin zarafin da ake yi musu, ciki har da Pauline wadda ta shafe tsawon shekara 10 tana fuskantar cin zarafi”, in ji Owoba.

Pauline na da ‘ya’ya uku tare da mutumin.

Sannan kuma ta ce Noko ya yi mata barazana ita da sauran ma’aikatan gidanta uku idan suka kuskura suka ce za su bayar da shaidar abin da ya farun a gaban kotu.

www.nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp