Wata babbar kotun Akure da ke Jihar Ondo ta saurari shari’ar wani mutum mai shekaru 50, Daniyan bayan ya rufe matarsa, Dorcas a daki sannan ya banka mata wuta.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, matar ta rasa ranta ne sakamakon mummunar kunar da ta samu bayan an fito da ita an kai ta asibiti inda ta kwashe kwana 3, daga bisani ta ce ga garin ku nan.
Wata majiya daga ‘yan uwan ta sun bayyana yadda mijin ya dauki wannan mummunan matakin, bayan samun labari a kan cewa ta siya wata kadara ba da sanin sa ba.
Sai dai mai gabatar da kara, H. M Falowo, ya ce, a na zargin mutumin da kisan kai. Sannan a na zargin Daniyan da kin barin matar ta tsere, bayan ya banka mata wuta ta hanyar rufe mata kofa.