Majalisar wakilai ta musanta zargin da ke cewa kowane ɗan majalisa ya karɓi naira miliyan 100 daga gwamnatin tarayya a matsayin kuɗin rage raɗaɗi cire tallafi.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi, ya fitar ya bayyana iƙirarin – da mataimakin sakataren gamayyar ƙungiyar ƙwadogon ƙasar NLC, Christopher Onyeka ya yi – a matsayin zargi marar tushe.
Mista Onyeka ya yi zargin cewa kowane ɗan majalisa ya karɓi naira miliyan 100 daga gwamnatin tarayya a matsayin tallafin rage raɗaɗi.
Sanarwar ta Mista Rotimi, ta kuma buƙaci mataimakin sakataren NLC da ya fito ya nemi afuwar majalisar a bainar jama’a
”NLC a matsayinta na mai faɗa-a-ji a Najeriya ka iya rasa kimarta, idan aka same ta da amfani da ƙarya a cikin gwagarmayarta”, in ji sanarwar.
“Muna so mu bayyana cewa Mista Onyeka ya yi ƙarya a cikin iƙirarin nasa, domin kuwa babu inda ‘yan majalisa suka karɓi wani kuɗi daga ɓangaren zartarwa a matsayin kudin rage raɗaɗi, saboda haka mun ɗauki wannan iƙirari a matsayin zargi marar tushe kuma abu ne da bai kamata ba”
Mista Rotimi, ya ƙara da cewa “Muna so mu tunawa NLC da duka ‘yan Najeriya cewa a cikin ƙasa da kwana 100 da ƙaddamar da majalisarmu ta 10, majalisar ta yi ƙoƙari wajen inganta jin daɗi da walwalar ma’aikata da sauran Najeriya”.


