Hukumar ƙididdiga ta kasa (NBS), ta ce, an samu ƙaruwar farashin kayayyakin da ake fitarwa zuwa ƙasashen ƙetare da kashi 46 cikin ɗari.
Alƙaluman na watanni uku na farkon shekarar 2024, sun nuna cewa ana ta fita da kayayyakin da kuɗinsu ya kai naira biliyan 31.
Idan aka kwatanta da irin wannan lokacin na shekarar 2023, an samu ƙaruwar kayayyakin da ake fitar da shi da kashi 145 cikin ɗari.
Alƙaluman sun nuna cewa, ana fitar da kayayayyaki da kashi 60 da ɗoriya cikin ɗari na cinikayya a kasar nan wanda ake kai su zuwa ƙasashen waje, wanda kuɗinsu ya kai sama da naira biliyan 19.
Ɗanyen mai shi ne ke kan gaba a kayan da ake fitar da su, wanda shi ne kashi 80 cikin ɗari, sai wasu kayayyaki da suka kai kashi 19 cikin dari.
Kasar nan dai ta dogara ne da ɗanyen mai wajen samun kuɗin shiga, duk da ƙoƙarin da ta ce, tana yi na bunƙasa sauran hanyoyin, wanda har yanzu bai taka kara ya karya ba.