fidelitybank

Kayan cikin gida sun habaka da fiye da kashi 3 a Najeriya – NBS

Date:

Hukumar ƙididdiga ta kasa National Bureau of Statistics (NBS), ta ce, jumillar abin da Najeriya take samarwa da ake kira Gross Domestic Product (GDP) ya haɓaka da kashi 3.98 cikin 100 a wata ukun ƙarshe na 2021.

Wani rahoto da hukumar ta fitar a jiya Alhamis ya ce hakan na nuna cewa tattalin arzikin na kan hanyar da ta dace idan aka kwatanta da irin wannan lokacin na 2020.

“GDP ya haɓaka da kashi 3.98 cikin 100 cikin wata uku na karshe na 2021, abin da ke nufin alamun samun ci gaba a wata uku masu zuwa tun bayan annobar korona a 2020 lokacin da samar da kayayyaki ya yi ƙasa da kashi 6.10 da kuma 3.62 a wata uku na biyu da na ukun 2020 sakamakon annobar,” a cewar rahoton.

Ya ƙara da cewa “haɓakar na nuna alamun ci gaba da warwarewar tattalin arziki, inda ya kai kashi 3.40 a 20221”.

Kazalika, sakamakon na wata ukun ƙarshe a 2021 ya zarta na 0.11 da aka samu a irin wannan lokaci na 2020, sannan ya yi ƙasa da wanda aka samu a wata uku na uku a 2021 (maki 0.05).

Rahoton ya ce jumillar kayayyakin da ‘yan Najeriya ke samarwa ya zuwa wata ukun na ƙarshe a 2021 ya kai triliyan 49 – N49,276,018.23. In ji BBC.

nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp