Kimanin ma’aikata da marasa lafiya 400 ne suka maƙale a cikin asibitin da sojojin Rasha suka kwace iko da shi a Kudancin birnin Mariupol.
Iryna Vereshchuk, mataimakin firaiministan Ukraine, ya ce, sojojin Rasha na ci gaba da harbin dakarun Ukraine daga cikin harabar asibitin.
Wakilin Yanayi a Mariupol na dada kamari yayin da mazauna garin kusan 400,000 ke fama da rashin ruwa da wutar lantarki da iskar gas, kuma ba su da halin barin garin. Samun mutanen da ke zaune a garin na da matukar wahala.
Dmytro Horshakov ya ce mahaifiyarsa mai shekaru 57 ta na asibitin kuma ya kasa samunta a waya, amma yana samun labarinta daga wani abokin shi da ke zaune a garin.