Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp na son a sake wasan gasar Firimiya da ya gudana ranar Asabar tsakanin ƙungiyarsa ta Liverpool da Tottenham.
Tottenham ce ta yi nasarar cin 2-1 a karawar ta mako na bakwai da Liverpool ta kammala fafatawar da ‘yan kwallo tara a cikin fili.
Klopp ya bukaci a sake wasan ne bayan da alkalan da suka kula da na’urar VAR suka yi kuskuren soke kwallon da Luis Diaz ya ci, kan cewar an yi satar gida.
Darren England da Dan Cook ne suka kula da VAR a karawar da kungiyar Anfield ta ci gida daf da za a tashi ta hannun Joel Matip.
”Wani abu makamancin haka bai kamata ya faru ba a gasar Firimiya, saboda haka nake tunanin ya dace a sake wasan.” in ji Klopp.
To sai dai BBC ta fahimci cewar hukumar da ke kula da gasar ta Firimiya ba ta da wata madogarar da za ta amince a sake wasan, sannan babu tabbas ko Liverpool ta rubuta bukatar hakan a rubuce.
Wadanda suka tafka kuskuren a wasan na Tottenham da Liverpool ba sa cikin alkalan wasan da za su yi alƙalanci a wasannin gasar Firimiya da za a buga a karshen makon nan.
Inda aka bukaci England da Cook da su hutu, sakamakon kuskuren da suka tafka a karawar ta hamayya.
Wadanda suka hura wasan na Tottenham da Liverpool, Simon Hooper shi ne zai kula da VAR a fafatawar Bournmouth da za ta je gidan Everton ranar Asabar.
Shi kuwa Michael Oliver, wanda shi ne ya yi jiran ko-ta-kwana zai ja ragamar karawa biyu a karshen makon.