Gwamnatin jihar Katsina ta ce, ta ware guraben karatu 40 ga ɗalibai ƴan asalin jihar waɗanda za ta tura ƙasar Masar domin karatu a fannin likitanci.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne a lokacin taron majalisar zartarwar jihar wanda gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya jagoranta.
Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Farfesa Abdulhamid Ahmed ya ce “ƙananan hukumomi 31 za su bayar da sunayen dalibai ɗai-ɗaya, yayin da garuruwan Daura da Funtua kuma za su bayar da sunayen dalibai bibbiyu. Inda za a zaɓi ɗalibai uku a cikin ƙwaryar birnin Katsina.
Kwamishinan ya ce “ɗaliban da suka kammala makarantun gwamnati ne kaɗai za a ɗauka, kuma shirin tura ɗaliban na da nufin samar da ƙwararrun likitocin da za a ɗauka aiki a cibiyoyin kiwon lafiya na jihar Katsina.