Kungiyar Katsina United ta samu tikitin shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta Najeriya (NNL) Super 8 bayan ta doke NAF 3-1.
Kungiyar Chanji Boys ita ce kungiya ta farko da ta samu wannan nasara inda saura wasanni biyu a jere.
Tawagar Usman Abdallah dai ba a doke su ba a gasar ta NNL a bana kuma sun samu maki 20 daga cikin 24 da ake iya samu.
Tawagogi hudu daga Kudu da Arewa ne za su fafata a gasar Super 8
Kungiyoyin hudu da ke kan gaba a gasar za su samu damar zuwa gasar Premier ta Najeriya (NPFL).
Katsina United dai ta fice daga gasar NPFL a kakar wasan data gabata.