Kungiyar Katsina United ta daukaka kara kan tarar da hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta ci tarar kungiyar.
An ci tarar Chanji Boys nera miliyan daya saboda rashin samar da isasshen tsaro a karawarsu ta biyar da Sunshine Stars a karshen makon jiya.
Katsina United ta bayyana hakan ne a wata takarda da shugaban kwamitin riko na kasa Kabir Dan’lami Rimi ya rubuta wa NPFL.
Dan Lami ya roki shugabannin NPFL da su sake duba takunkumin da aka kakabawa kungiyar saboda babu abin da ya faru a lokacin wasan.
Ya kuma tabbatar da cewa kungiyar za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa don ganin an aiwatar da isassun matakan tsaro.
An umurci Katsina United da ta biya tarar cikin kwanaki 14 ko kuma ta yi kasada da karin takunkumi har sai an amsa karar.