Victor Mbaoma ya fara da kafar dama bayan Katsina United ta doke DMD FC da ci 2-1 a gasar cin kofin Super 8 da suka yi a Najeriya.
Mbaoma ya ci wa Chanji Boys kwallo a minti na 14 da 20 bi da bi.
Dan wasan ya shiga kungiyar ta Usman Abdallah ne bayan ya yi rashin nasara da kungiyar Mouloudia d’Algiers ta Algeria.
Katsina United za ta kara da EFCC a wasansu na biyu ranar Litinin.
Nasarar da kulob din zai yi zai sa kulob din ya koma gasar Premier ta Najeriya.