fidelitybank

Katsina: Ba za mu bari sabuwar gwamnati ta gaji matsalar tsaro ba – Masari

Date:

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya tabbatar da cewa yadda gwamnatin sa ta gaji matsalar tsaro a gwamnatin da ta gabata, insha Allahu ba za su yarda gwamnatin da za ta zo ta gaji matsalar ba.

Gwamna, Aminu Bello Masari ya bayyana hakan a yau Laraba 22-12-2021 a fadar gwamnatin jihar ta Janar Muhammadu Buhari, a lokacin da ya rattaba hannu a kan kasafin 2022.

Gwamnan ya kara da cewa”Duk da kalubalen tsaro da ake ta fuskanta tsawon lokaci da kuma irin kudaden da hakan ke ci, gwamnati ta yi iya kokarin ta wajen samar da ababen more rayuwa ga al’umma, musamman na karkara. wannan kasafin kudi ya maida hankali ne wajen kammala duk ayyukan da wannan gwamnati take kan yi, illa wasu kalilan masu muhimmanci da za a yi”.

“Aiwatar da wannan kasafin kudi sau da kafa ya na da matukar muhimmanci ga wannan gwamnati da kuma jam’iyyar APC, domin shi ne na karshe da za a aiwatar har zuwa karshen shekarar, na shekarar 2023”. Inji Masari.

Ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa, musamman masu sha’awar yin takara, da su sa ni cewa Allah ba ya yin sabon aiki, duk wanda zai baiwa ya riga ya gama. Saboda haka wajibi ne ayi wannan hidima cikin bin doka da oda, tare da nuna ‘yan uwantaka domin samun nasarar jam’iyyar da kuma zaman lafiya da cigaban jihar.

Ya kuma yaba wa ‘yan majalisar saboda yadda su ka sadaukarwa da jajircewa wajen kammala tantance kasafin kudin cikin kwanaki talatin da biyar (35) da gabatar da shi a zauren majalisar.

Tun farko a nashi jawabin, shugaban majalisar dokokin jihar, Tasi’u Maigari Zango ya bayyana cewa, Majalisar ta yi nazari kwarai tare da tsantseni kan kasafin kudin, ta dalilin haka ne ma, ta gabatarwa wa Gwamnan Naira Biliyan Dari Ukku da Ashirin da Ukku, da Miliyan Dari Biyu da Tis’in da Shidda, da Dubu Dari Biyu da Ashirin da kuma Dari Shidda da Sittin da Daya(N323,296,220,961) kasa da Naira Biliyan Dari Ukku da Arba’in, da Miliyan Dari Tara da Hamsin da Daya da Dubu Dari Tara da Goma Sha Biyu da Dari Biyar Hamsin da Bakwai (N340,951,912,557) da tun farko Gwamnan ya gabatar a gaban zauren Majalisar.

www.nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp