Lalacewar wayoyin ƙarƙashin teku a sassan gabashi da yammacin Afirka lamarin ya sa ƙasashen Afirka da dama fuskantar gagarumar matsalar katsewar sadarwar intanet a ranar Alhamis.
Afirka ta Kudu da Najeriya da Ivory Coast da Laberiya da Ghana da Burkina Faso na cikin ƙasashen da suka fuskanci yankewar intanet ɗin.
Hukumar sadarwa ta Najeriya ta tabbatar da katsewar. Cikin wata sanarwa, NCC ta ce wayoyin da abin ya shafa sun taso ne daga Turai suka bi ta Gaɓar ruwan gashin Afirka.
Sun yanke ne a tekun maliya lamarin da ya shafi sauran wayoyin da ke haɗe da su a ƙarƙashin tekun.
“Kamfanonin wayoyin – WACS da ACE a gaɓar ruwan yammacin Afirka daga Turai sun fuskanci matsala.
NCC ta ƙara da cewa yankewar wayoyin ta sa an samu matsalar katsewar intanet a Najeriya da wasu ƙasashen yammacin Afirka sannan ƙarfin network na kamfanonin sadarwa ma ya fuskanci targarɗa a ƙasashen.
Shugaban ƙungiyar kamfanonin sadarwa a Najeriya Gbenga Adebayo ya tabbatar da matsalar da wayoyin ƙarƙashin tekun suka samu a tekun maliya.
MTN, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa a Najeriya ya fitar da sanarwa inda ya nemi afuwar abokan hulɗarsa saboda rashin ƙarfin network da suke fuskanta.
Shi ma ya ce hakan ta faru sakamakon lalacewar wasu sayoyin ƙarƙashin teku a sassan gabashi da yammacin Afirka.
Wasu bankuna a Najeriya suma sun nemi afuwar abokan hulɗarsu saboda matsalar da suka fuskanta. In ji BBC.
A Ivory Coast, ƙarfin sadarwar intanet ya ragu zuwa kashi huɗu cikin ɗari da safiyar ranar Alhamis a cewar Netblocks, kamfanin da ke bibiyar ƙarfin intanet.
A Laberiya ma ƙarfin intanet ɗin ya ragu zuwa kashi 17 cikin 100, a Benin kuma ya tsaya kan kashi 14 sai Ghana da kashi 25 kamar yadda Netblocks ya nuna.